Honore Traore ne sabon shugaban Burkina | Labarai | DW | 31.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Honore Traore ne sabon shugaban Burkina

Hafsan hafsoshin Burkina Faso Honore Traore ya hau madafun ikon kasar bayan da Blaise Compaore ya yi murabus sakamakon adawar 'yan kasa, bisa kudurinsa na kara wa'adi.

Compaore wanda ya dare mulkin kasar bayan juyin mulki a shekara ta 1987 ya yi kokarin yin watsi da bukatar al'umma na ya yi murabus inda har suka yi zanga-zanga suka kona majalisar dokoki da wasu kafafen yada labarai.

A wata sanarwar da ya rubuta ya sanyawa hannu, Compaore ya ce ya ajiye mukamin ne da nufin ganin ya bude hanyar gudanarda zabe mai tsabta nan da kwanaki 90.

Mutane sun yi ta rawa kan tituna suna murna bayan da aka karanto sanarwar tsohon shugaban a gidan talabijin na kasa. Sai dai murnar ta dan lafa da suka ga cewa hafsan hafsoshin ne ya karbi mukamin mafi girma na kasar.

A karkashin kundin tsarin mulkin Burkina Faso, shugaban majalisar dokoki ne ya kamta ya karbi iko idan shugaba ya yi murabus amma kuma tun jiya alhamis aka rusa majalisar dokokin