1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hizbollah ta maida wa Isra'ila martani

August 25, 2019

Kungiyar nan ta Hizbollah, ta maida martani kan hari da jirage marasa matuka da Isra'ila ta kai kan 'ya'yanta a Labanan, tana mai bayyana hakan a matsayin takalar fada.

https://p.dw.com/p/3OSn3
Hassan Nasrallah
Hoto: picture alliance/AP/H. Malla

Jagoran kungiyar ta Hizbollah Sheikh Hassan Nasrallah, ya ce harin da jirage marasa matuka mallakin Isra'ilar suka kai wani yanki na Beirut na kasar Labanan wani hadari ne babba. Kungiyar ta ce harin ya lalata tashar watsa labarunta da ke a kudancin birnin na Beirut.

Tun da farko Firaministan kasar Labanan Saad Hariri ya bayyana harin na Isra'ila a matsayin wani kokari ne na haddasa husuma tsakanin kasashe. Iran dai na goyon bayan kungiyar da 'ya'yanta ne galibin mazauna a Beirut.

Harin na kuma zuwa ne bayan dakarun Isra'ila sun ce wani jirginsu ya kai hari kan sojojin Iran da mayakan tawayen Shi'a, a kusa da Damascus babban birnin kasar Siriya. Jagoran na Hisbollah Hassan Nasrallah ya ce harin na Siriya ya kashe masa mutane biyu.