Hissene Habre na Chadi ya daukaka kara | Labarai | DW | 12.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hissene Habre na Chadi ya daukaka kara

Hissene Habre da kotun musamman ta Afirka da ke hukunta manyan laifuka ta yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Hissene Habre yayin yanke masa hukunci a kotu

Hissene Habre yayin yanke masa hukunci a kotu

A karshen watan Mayun da ya gabata ne dai kotun ta ce ta samu tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Chadi Habre mai kimanin shekaru 73 a duniya, da laifin aikata kisa da cin zarafin dan Adam a yayin mulkinsa.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam ma dai sun zargi Habre da laifin kashe wasu mutane 40,000 a yayin mulkin nasa daga shekara ta 1982 zuwa 1990. Shari'ar ta Habre da aka gudanar a Dakar na Senegal ta dauki hankulan al'ummomin kasashen duniya musamman ma na Afirka da ke ganin watakila hukuncin zai sa shugabannin Afirka da ke da akida irin tasa su shiga hankulansu.