Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
An zargi Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da neman yin katsalandan a shugabancin Kano
Sabon gwamnan kano da ya sha rantsuwar kama aiki Abba Kabir Yusuf ya ce gamnatinsa ta gaji dibin bashi daga gwamnatin da ke barin gado ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sabuwar gwamnatin Kano ta umurci hukumomin da ke karkashinta su tabbatar sun rusa gine-ginen da aka yi a filayen masallatai da makabartu da asibitoci da wurin shakatawar yara da kuma kasuwanni.
Engr. Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya lashe zaben gwamnan jihar Kano inda ya ka da abokin hamaiyarsa na APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna. Tuni dan takarar APC din ya yi wa sabon zababben gwamnan fatan alheri.
Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi watsi da zargin da wasu ke yi, na shirya yi wa zababben gwamnan jihar Kano katsalandan a harkokin shugabancin Kano.