Himma dai Matasa: Mai sana′ar danwake | Himma dai Matasa | DW | 03.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Himma dai Matasa: Mai sana'ar danwake

Aisha Ibrahim Matashiya ce Mai shekara 22 a duniya, ta kammala karatunta na diploma a fannin nazarin tattalin arziki da gudanarwa, wato "Economics and Management" da Turancin Ingilishi, ta kama sana'ar danwake.

Nigeria HdM Kaduna Danwake

Matashiya mai sana'ar danwake

Matashiyar ta rumgumi sana'ar yin danwake wadda ta taimaka mata matuka a rayuwa. Aisha Ibrahim dai ta riki sana'ar yin danwaken a matsayin rufin asiri bayan da kamala karatunta na karamar diploma a fannin nazarin tattalin arziki da gudanarwa, shin ko ya aka yi ta kama wannan sana'ar? Shigowar wasu sababbin kayayyaki na zamani sun saka ta kara kawata danwaken a cewarta.

Ya dai danganta da man da kake bukata wato man gyada ko manja, matashiyar ta ci gaba da cewa a lokutan baya a kan sayar da danwake da safe domin karin kumallo ko kuma abincin rana wasu kuma su saya da maraice, amma a yanzu ko yaushe kazo za a jefa maka. A gefe guda da dama daga cikin matasan kan yiwa sana'ar gani-gani. Aisha ta ce a kan ci karo da kalubale jefi-jefi, domin duk hannun da ya kirga riba watarana zai kirga faduwa.

Sai dai babbar nasarar da matashiyar ta samu kuma take alfahari da ita bai wuce batun karatunta da ta kammala ba tare da gudummawar da mahaifiyarta da kanwarta suka bayar a kan wannan sana'ar. Ta kuma bayyana cewa babban burinta shi ne samun wani katafaren wuri da za ta bude domin sayar da danwaken, in har ta samu babban jari. A karshe ta yi kira ga matasa 'yan mata kan batun kama sana'a.

Sauti da bidiyo akan labarin