Hillary Clinton daTrump sun kara yin nasara | Labarai | DW | 16.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hillary Clinton daTrump sun kara yin nasara

'Yan takaran shugabancin kasar ta Amirka dai sun samu galaba ne a zaben fidda gwani da aka yi a jihohi da ke da mahimmanci a siyasar kasar

'Yar tarar shugabancin Amirka daga bangaren jam'iyar Demokrat ta kama hanyar samun tabbacin samun galaba kan abokanta a zabukan fidda gwani, hakan dai ya bayyana a daran jiya, inda Clinton ta lashe daukacin zabukan fidda gwani da aka yi a jihohin kasar hudu. Jihohin da aka yi zaben jiya sune Florida, Ohio, North Carolina, da Missouri. A bangaren jami'iyar Republikan Donald Trump ne ya yi nasara, ko da yake gwamna John Kasich ya lashe zaben a jiharsa ta Ohio. Shi kuwa Senator Marco Rubio, daya daga cikin yan takara bangaren Republikan ya ajiye takaransa bayan sakamakon na jiya.