1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Herzog ya taya Netanyahu murnar lashe zabe

Mohammad Nasiru AwalMarch 18, 2015

Bayan da bisa ga dukkan alamu shi ne ya yi nasara a zaben, Benjamin Netanyahu ya fara yunkurin kafa gwamanti cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/1Esha
Israel Wahlen 2015 Netanjahu Jubel
Hoto: Reuters/N. Elias

Mai kalubalantar Firaministan Israila, a zaben majalisar dokokin kasar, wato madugun adawa Jizchak Herzog ya amince ya sha kaye har ma ya mika sakon taya murna ga Firaminista Benjamin Netanyahu. Jam'iyyar Likud ke gaba a sakamakon wucin gadin da hukumar zabe ta fitar, wanda ya nuna cewa ta wuce hadakar jam'iyyar adawar ta Zionists Union da kusan kashi biyar cikin 100 na kuri'un da aka kada. Yanzu dai jam'iyyar ta Likud ta samu kujeru 30 daga cikin kujeru 120 na majalisar ta Knesset. A yayin da ita kuma hadakar jam'iyyun Zionists Union ta samu kujeru 24 sai kuma hadakar jam'iyyun Larabawa mai kujeru 14. Yanzu haka dai Netanyahu ya fara yunkurin kafa gwamanti cikin gaggawa, inda ya ce:

"Duk da matsaloli wannan babbar nasara ce ga jam'iyyar Likud. 'Yan Isra'ila sun zura mana ido mu kafa gwamnati da za ta yi musu aiki, abin da kuma za mu yi kenan."

Jam'iyyarsa ta Likud ta ce nan da makonni biyu za a samu sabuwar gwamnatin kawance.