Hatsari na neman rikidewa ga adawa da gwamnati
May 15, 2014Talla
A yanzu haka dai fatan samun wani da rai a cikin ramin hakar ma'adinai na kara dushewa, daga mahakar gawoyin kwal a garin Soma da ke yammacin kasar ta Turkiya. Akalla mutane 282 suka rasu, bayan gobara da fashewar wasu sinadarai, abinda ya sa wannan ya kasance hatsiri mafi muni a tarihin masana'antun Turkiyan. A jiya dai dubban mutane ne suka yi arangama da 'yan sanda a biranen Ankara da Instanbul, inda suke zargin gwamnanti da kuma ma'aikatun hakar ma'adinan da sakaci.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu