Harin ′yan bindiga kan sojojin Burundi | Labarai | DW | 11.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin 'yan bindiga kan sojojin Burundi

Rundunar sojojin Burundi ta ce 12 daga cikin maharan da suka kai hari a sansanonin sojojin kasar uku, a kokarin da suke na sace makamai tare da sakin firsunoni 'yan uwanasu sun sheka barzahu.

'Yan bindiga sun kai hari a kan sojojin Burundi

'Yan bindiga sun kai hari a kan sojojin Burundi

Mazauna birnin Bujumbura sun ji karar bindigogi da kuma ta abubuwa masu fashewa a yayin artabu tsakanin jami'an sojojin kasar da kuma 'yan bindigar da suka kai harin. A wani jawabi da ya yi a gidan radiyon kasar, kakakin rundunar sojojin Kanal Gaspard Baratuza ya bayyana cewa kawo yanzu sun cafke maharan guda 20, kana daga cikinsu akwai wani wanda ya samu raunuka da a yanzu haka yake karbar magani a asibitin sojojin. Baratuza ya kara da cewa akwai wasu sojoji guda biyar da suka samu raunuka a yayin bata kashin.