Harin ta′addanci ya hallaka dan sanda a Faransa | Labarai | DW | 21.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci ya hallaka dan sanda a Faransa

Jami'an tsaron Faransa sun hallaka dan ta'adda da ya kai hari birnin Paris tare hallaka dan sanda daya sannan wasu biyu suka samu raunika.Wannan hari ya zo ne daf da lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa.

'Yan sanda a Faransa sun bindige dan ta'adda da ya kai hari kan birnin Paris fadar gwamnatin kasar, abin da ya janyo mutuwar dan sanda daya, sannan wasu biyu suka samu raunika. Jami'an tsaron suna da masaniya kan dan ta'addan da ya kai harin a Champs Elysees daya daga cikin wuraren masu tasiri a birnin Paris. Maharin ya bude wuta jim kadan bayan ya fito daga cikin motar da ya tuka zuwa wajen, kuma 'yan sanda sun hallaka shi lokacin da ya yi yunkurin tserewa.Tuni Shugaba Francois Hollande ya nuna takaici bisa harin na ta'addanci sannan ya kira taron majalisar tsaro.Tun shekara 2015 kasar ta Faransa ke karkashin dokar ta baci sakamakon hare-hare tsageru masu kaifin kishin addinin Islama da suka janyo mutuwar kimanin mutane 230.