Harin ta′addanci a Kabul | Labarai | DW | 06.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a Kabul

A cewar hukumomin Afganistan wasu mutane dauke da makamai sun kaddamar da hari a safiyar wannan Talata a cibiyar kungiyar agaji ta Care International da ke babban birnin kasar

Sa'o'i kalilan bayan wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da wasu 'yan kunar bakin wake, sai Kungiyar Taliban ta ce sune suka kai harin wanda ya auku a harabar ofishin ministan tsaro da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 24 a yayinda wasu 91 suka ji rauni.

Sai dai ministan cikin gida na kasar Sediq Seddiqqi ya sanar a shafinsa na twitter cewa sun yi nasarar bindige mutanen da suka kai hari na safiyar yau bayan share awoyi ana musayar wuta da su.

Ya kuma kara da cewa wasu mutane shida sun ji rauni kana an yi nasarar tsira da wasu mutanen 31. A halin yanzu kuma sun dauki matakin hana zirga-zirga a unguwanni da dama na birnin na Kabul dama rufe makarantu.