1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci a Faransa ya hallaka mutum guda

Suleiman Babayo
March 23, 2018

Mutum guda ya mutu sakamakon harin ta'addanci a garin Trebes na yankin kudancin Faransa tare da garkuwa da mutane.

https://p.dw.com/p/2uqpx

Hukumomin kasar Faransa sun bayyana harin da aka kai kan wani katafaren shago da ke kudancin kasar a matsayin wani lamarin ta'addanci, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce. Yanzu haka 'yan sanda sun kewaye shagon inda 'yan bindiga da ba a tantance ba ke garkuwa da mutane a garin na Trebes.

Sai dai wata majiyar 'yan sanda ta ce kimanin mutane takwas aka yi garkuwa da su, inda tuni kwararru kan ta'adanci suka bude bincike. Shugaba Emmanuel Macron na kasar ta Faransa ya bayar da umurni ga mnistan harkokin cikin gida ya garzaya zuwa garin da 'yan ta'addan ke dauke da makamai suke garkuwa da mutane.

Magajin garin na Trebes ya shaida wa wata kafar yada labarai cewa maharin shi daya ne, kana an samu nasarar sanin daukacin mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma mutum guda ya mutu.