Harin kunar bakin wake ya hallaka wasu dakarun Libiya
March 17, 2014Akalla dai gawawaki biyar ne aka kai babban asibitin birnin, tare da sauran sassan jikin mutanen da suka tarwatse, da kuma wadanda suka ji rauni sakamakon harin.
A cewar wata majiya ta sojan kasar, motar dai ta kasance a tsaye kusa da barikin, amma kuma ta tarwatse yayin da wani gungun sojoji ke fitowa, daga barikin.
Birnin Benghazi ne dai cibiyar tashe-tashen hankullan da ya haddasa kawar da gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi, inda a halin yanzu wannan birni yake a matsayin wani filin daga, inda ake yawan kai hare-hare ga jamiyan tsaro na yan sanda ko kuma soja.
A ranar 22 ga watan Disamban da ya gabata, harin kunar bakin waken yayi sanadiyar mutuwar wasu jami'an tsaron a nisan km 50 da birnin da Benghazi.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe.