Harin kunar bakin wake kan ′yan kungiyar IS | Labarai | DW | 05.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake kan 'yan kungiyar IS

Wata mata ta tada bam da ta sanya a jikinta daidai inda 'yan kungiyar nan ta IS suke a garin Kobani da ke kan iyakar Siriya da Turkiyya.

Hukumar da ke sanya idanu kan kare hakkin dan Adam a Siriya wato Syrian Observatory for Human Rights ta ce matar ta tada bam din ne a gabashin garin na Kobani inda 'yan IS da ke son karbe garin suka ja daga kuma harin ya hallaka 'yan kungiyar da dama.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance yawan wanda suka rasu ko suka jikkata ba. Wannan dai shi ne karon farko da Kurdawa musamman ma dai mace ta kai harin kunar bakin wake kan 'yan kungiyar ta IS.