Harin kunar bakin wake a kan Coci a Pakistan | Labarai | DW | 17.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a kan Coci a Pakistan

Akalla mutane guda takwas suka mutu biyu daga cikinsu mata kana wasu 30 suka jikkata a sanadiyyar harin kunar bakin wake da wasu 'yan bindiga suka kai a kan wata Coci da ke a kudu maso yamacin Pakistan.

'Yan bindigar guda biyu sun kai harin ne a garin Quetta da ke cikin lardin Balouchistan. Ministan cikin gida na yanki ya ce 'yan sanda sun harbe daya dan kunar bakin wake a lokacin da yake kokarin shiga Cocin. Amma daya ya yi nasarar kutsa kai cikin Cocin ya kuma tayar da bam a lokacin da mabiya ke yin aiki ibada na ranar Lahadi.