Harin kunar bakin wake a Kamaru | Labarai | DW | 01.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Kamaru

An ba da rahoton cewar wasu mata 'yan kunar bakin wake guda hudu sun tarwatsa kan su da bama-bamai da ke a jikin su a garin Mora da ke yankin arewa mai nisa na Kamaru.

Wata majiyar rundunar sojojin kasar ta Kamaru ta ce matan guda hudu da ke dauke da jigidar abubuwan da ke fashewa sun yi yunkurin shiga garin na Mora a lokacin da 'yan banga suka gano su, suka tayar da bama-baman da ke a jinkin su daf da shigowar garin. Garin na Mora da ke a arewacin Kamarun a nan ne aka jibge dakarun rundunar hadin gwiwa na kasa da kasa FMM da ke yaki da kungiyar Boko Haram.