Harin kunar bakin wake a birnin Sanaa na Yemen | Labarai | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a birnin Sanaa na Yemen

Wani dan kunar bakin wake a mota makare da bama-bamai yayi sanadin halaka mutane sama da talatin a gaban wata kwalejin 'yan sanda a birnin Sanaa na kasar Yemen,

Dan kunar bakin waken dai ya halaka wadannan mutane ne a yayin da aka samu dandazon mutane da suka tattaru a gaban ginin wannan kwaleji, a wani aikin daukar sabbin jami'ai kamar yadda jami'an tsaro suka bayyana.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki bayan da wani harin bam ya halaka wasu 'yan shi'a shida masu dauke da makamai a ranar Litinin, yayin da wani harin a ranar Lahadi ya kashe wasu hudu ciki kuwa har da wani dan jarida a birnin Dhamar da ke zama mai yawan mabiya shi'a.

Kasar ta Yemen dai ta shiga cikin halin tsaka mai wuya tun bayan zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin Ali Abdallah Saleh a shekarar 2012.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu