Harin kunar bakin wake a Arewacin Bagadaza | Labarai | DW | 25.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake a Arewacin Bagadaza

Mutane tara ne suka rasu a wani harin kunar bakin wake da aka kai da yammacin wannan Alhamis a wani masallacin, 'yan Shi'a da ke Arewa maso Yammacin Bagadaza.

Wani daga cikin manyan jami'an 'yan sandan kasar ta Iraki ya sanar cewa, wasu mutane ne 'yan kunar bakin wake guda biyu suka tarwatsa kansu a gaban Masallacin, a unguwar Al-Shaala inda nan take mutane tara suka rasu wasu kuma 22 suka jikata cikinsu har da wani jami'in 'yan sanda.