1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka jama'a a yayin wani harin Boko Haram

Abdoulaye Mamane Amadou
March 1, 2020

Boko Haram ta hallaka mutane 10 tare da kokkona gidajen jama'a a kauyen Rumirgo na cikin jihar Borno Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Yhkk
Nigeria Bilabulin Village | Einwohner sitzen an einem abgebrannten Haus nach einem Angriff von Boko Haram
Hoto: Reuters/K. Adewale

Rahotanni daga kauyen Rumirgo sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram kan motoci dauke da bindigogi sun dinga yin harbin kan mai uwa da wabi tare da kwasar kayayakin abinci bayan jama'a sun gudu don tsira da ransu daga garin.

Wani shedun gani da ido kuma dan kato da gora mai suna Peter Malgwui, ya tabbatarwa manema labarai cewa mayakn sun shake manyan motoci biyu da kayan cimaka da suka sata a garin bayan jama'a sun gudu, kana daga bisani suka koma a cikin dajin Sambisa da ke zaman tungar mayakan kungiyar.