Harin Boko Haram a Jihar Adamawa ta Najeriya
October 19, 2015Talla
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA da ta tabbatar da wannan labarin ta ce an kai harin ne a karshen mako sai dai ba ta yi karin haske ba dangane da lamarin ba.
Wadanda suka shaida faruwar wannan lamari dai sun ce mutane bakwai daga cikin mutanen sun rasu ne bayan da wasu mata biyu suka tada bam din da yake jikinsu, yayin da sauran kuma suka gamu da ajalinsu sanadiyyar harbi da bindiga da aka yi musu.
Jihar Adamawa dai tana daga cikin jihohin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya da tada kayar bayan 'yan kungiyar ta Boko Haram ke shafa, batun da ya yi sanadin rasuwa dubban mutane.