Harin bindiga a tsahar jirgin kasa a Holland | Labarai | DW | 18.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bindiga a tsahar jirgin kasa a Holland

A cewar jami'an 'yan sandan, harin da aka kai a birnin Utrecht shi ya zaburar da mahukunta daukar matakai na tsaurara tsaro .

Kasar Holland ta tsaurara matakan tsaro a filayen tashi da saukar jiragen sama na kasar da ma wasu manyan gine-gine bayan da wani dan bundiga ya bude wuta a tashar jirgin kasa da ma kisan mutane guda uku baya ga wasu da dama da suka samu raunika kamar yadda jami'an 'yan sanda a kasar suka bayyana.

A cewar jami'an 'yan sandan, harin da aka kai a birnin Utrecht shi ya zaburar da mahukunta daukar matakai na tsaurara tsaro a manyan gine ginen a kasar ta Holland.