Harin bam ya hallaka sojojin Masar bakwai | Labarai | DW | 19.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin bam ya hallaka sojojin Masar bakwai

Tashe-tashen hankali na ci gaba da ritsawa da yankin Sinai na kasar Masar. Ana kyautata zaton cewar masu kaifin kishin Islama sun dana bam da ya hallaka sojoji.

Wani bam da aka dana a gefen hanya ya hallaka sojojin kasar Masar bakwai, tare da jikata wasu hudu cikin yankin Sinai mai fama da tashe-tashen hankula.

Jami'ai sun ce bam ya tarwatse lokacin da motocin yakin sojoji ke wucewa, wadanda ke sintirin aikin tsaro na bututun gas. Ana samun tashin hankali a yankin na arewacin Sinai da ake dangantawa da masu kaifin kishin addinin Islama.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe