Wasu jami'an soji biyu na rundunar sojojin yankin tafkin Chadi sun rasa rayukansu a Mali bayan da motarsu ta taka wani bam da mayakan jihadi suka dana.
Harin ya auku ne a yankin Boulkessi, yankin da kungiyar Serma Katiba da ke da alaka da Al-Qaeda ke gudanar da ayyukanta a kasar Mali. Sojojin biyu na kasashen Chadi ne a cewar sanarwar da mai wakiltar Majalisar Dinkin Duniya a Mali Mahamat Saleh ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.
A yankin na Tafkin Chadi dai akwai rundunoni da dama da suke yaki da mayakan da ke gwagwarmaya da makamai ciki kuwa har da rundunar sojin Faransa ta Barkhane.