1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya kashe sama da mutane 20 a Adamawa

Zainab Mohammed Abubakar
May 1, 2018

Hare-haren guda biyu ya auku ne da a wannan Talata a kusa da wani masallaci da ke layin 'yan gwanjo a da ke cikin babbar kasuwar Mubi

https://p.dw.com/p/2wyIl
Maiduguri Nigeria Boko Haram Anschlag
Hoto: Reuters/A. Kingimi

A cewar majiyar 'yan sandan da ke Mubi, sama da mutane 20 ne biyu ne hare-haren suka ritsa da rayukansu daura da wasu masu yawa da suka jikkata.

Wadanda suka ganewa idanunsu sun shaidar da cewar, sun ga ana jigilar wadanda suka ji rauni da da wadanda suka rasa rayukansu zuwa babban asibitin gwamnati da ke garin Mubi.

A cewarsu dai wani abu mai kama da bam ya tarwatse a kusa da wani masallaci da ke layin 'yan gwanjo a kasuwar gabanin sallar Azahar. A yayin da na biyu ya sake tashi a lokacin da ake kokarin taimakawa wadanda suka jikkata a harin farkon

Duk da cewar babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na Mubi, Kungiyar Boko Haram ta kan kai hare-hare a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya ciki kuwa har da suka hada da Borno da Yobe da Adamawa.