Hari ya hallaka mutane da dama a Nafada | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka mutane da dama a Nafada

'Yan bindiga sun kashe wani shehun malami da dalibansa a wani hari da suka kai a karamar hukumar Nafada da ke jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Nafada da ke jihar Gombe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda suka hallaka jami'an tsaro da kuma wani shahararren malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Adamu Misira da almajiransa guda hudu.

Wani mazaunanin karamar hukumar ya shaida wa wakilinmu Al-Amin Muhammad ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun afkawa garin ne da misalin karfe daya da rabi na rana inda suka bude wuta tare da kona wani ofishin ‘yan sanda da kuma ofishin jam'iyyar PDP mai mulki.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka kai irin wannan hari a Nafada wanda ke kan iyakar jihohin Gombe da Yobe, lamarin da ya tada hankulan mutane garin, wadanda da yawa daga cikinsu suka fantsama dazuka don tsira da rayukan su.

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro ko kuma ita gwamnati jihar Gombe ko ta tarayya ba su ce komai kan wannan harin ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu