Hari ya hallaka mutane 12 a Faransa | Labarai | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka mutane 12 a Faransa

Shugaban Faransa Francois Hollande ya tabbatar da cewa harin ta'adanci kan wani gidan mujalla ya hallaka mutane 11

Jami'an kasar Faransa sun tabbatar da mutuwar mutane 11 bayan a wani gidan mujallar mai zanen barkwanji, cikin waddan suka hallaka akwai 'yan sanda biyu. Sannan akwai mutane uku da suka samu raunika.

Shugaba Francois Hollande ya ce babu makawa wannan hari na ta'adaci da aka kai wa mujallar ta Charlie Hebdo, lokacin da ya kai ziyara zuwa wajen da abin ya faru. Tuni Shugaba Hollande ya kira taron gaggawa, domin duba yanayin tsaro, dama an karfafa matakan tsaro a wuraren taruwan jama'a.

Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi kakkausar suka kan hari da aka kai na Faransa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu