Hari ya hallaka mutane 10 a Libiya | Labarai | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka mutane 10 a Libiya

Fiye da mutane 10 sun hallaka a harin da aka kai birnin Tripoli na kasar Libiya

Kimanin mutane 10 sun hallaka lokacin da 'yan bindiga suka kai hari wani otel da 'yan kasuwa da jami'an diflomasiya ke amfani da shi a birnin Tripoli na kasar Libiya. Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan kasashe ketere biyar da 'yan kasar biyar suka hallaka sakamakon harin.

Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka ta fada cikin rudanin siyasa da tattalin arzikin tun shekara ta 2011, bayan juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi, inda yanzu haka ake da gwamnatoci guda biyu masu ikirarin rike da madafun iko, duk da yunkurin da kasashen duniya suke yi na sasanta bangarorin biyu.