Hari ya hallaka fararen hula a Siriya | Labarai | DW | 29.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ya hallaka fararen hula a Siriya

Fararen hula akalla 16 ne suka mutu a sakamakon wani hari da aka kai kan tungar 'yan tawaye da ke a yankin Idlib, inda ake tsugune da dubban 'yan gudun hijira.

Ana dai zargin jiragen yakin gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Rasha da laifin kai harin a wani yunkuri da ta ke na ganin ta kwace ikon yankin na Idlib da ke karkashin ikon 'yan tawaye. Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights da ke rajin kare hakkin dan Adam mai mazauni a Birtaniya, ta ce ba ta kai ga tantance kasar da ke da alhakin kai harin ba.

Kasashen duniya sun yi tur da harin. Yankin na Idlib dai, ya kasance tungar karshe da ya rage karkashin ikon 'yan tawaye da gwamnati ke kokarin ganin ta kwace kafin ta yi shelar nasara a yakin da aka kwashi fiye da shekaru takwas ana gwabzawa a tsakanin bangaren gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad da 'yan tawayen.