Hari ta sama ya hallaka jagoran Al-ka′ida a Yemen | Labarai | DW | 05.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari ta sama ya hallaka jagoran Al-ka'ida a Yemen

Shawki al-Badani na zama gaba-gaba cikin wadanda Amirka ke zargin na da hannu a harin ofishin jakadancin Amirka da ke birnin Sanaa na Yemen a shekarar 2012.

Babban jami'i a kungiyar Al-ka'ida da Amurka ke nema ruwa a jallo, ya hallaka a wani harin jirgin sama mai tuka kansa da aka kai a daren jiya Talata, kamar yadda rahotanni suka nunar a ranar a safiyar yau Laraba.

A cewar majiyarmu, shi ma Nabil al-Dahab jagoran Ansar al-Sharia a Yemen a lardin al-Bayda ya rasu tare da wasu mambobin kungiyar guda hudu, ciki kuwa har da Shawki al-Badani wanda ya kasance jagoran kungiyar ta Al-ka'ida a mashigar tekun Arabiya..

Shi dai Al-badni Amirka na nemansa ne a matsayin babban dan ta'adda, saboda sanya hannunsa a wasu shirye-shiryen kai farmaki ga ofishin jakadancin Amirka da ke Sanaa babban birnin kasar ta Yemen a shekarar 2012, harin bam din kuma da ya yi sanadin kisan sama da sojoji 100.