1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta yi asaran sojinta

Usman Shehu Usman
May 27, 2019

Akalla wasu jami'an sojin Chadi hudu da wani dan jarida suka mutu, bayan da motar da suke ciki ta tarwatse a kan hanyar kai dauki ga wasu sojojin da Boko Haram suka afka wa

https://p.dw.com/p/3J71K
Afrika Nigeria Niger & Tschad Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/E. Braun

Rahotannin sun ce sojojin na kan hanyarsu ne i zuwa wani sansanin sojojin Chadi da Boko Haram suka kai wa hari a daran Juma'a. Sansanin sojojin dai na dab da tabkin Chadi, inda rahotannin suka tabbatar sojojin Chadi sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram 23, yayin da su kuma suka rasa soja guda. A 'yan kwanakinnan dai kungiyar Boko Haram ta tsananta yin amfani da dasa boma-bamai kan hanya, inda hakan ke yin sanadin mutuwar sojoji da fararen hula a yankunan Chadi da Najeriya.