1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun hallaka yayin wani hari a Pakistan

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 13, 2016

A kallah mutane 15 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani harin bom da aka kai a kan jami'an 'yan sanda a kasar Pakistan.

https://p.dw.com/p/1HcGo
Ma'aikatan Polio na fuskantar barazana a Pakistan
Ma'aikatan Polio na fuskantar barazana a PakistanHoto: Getty Images/AFP/A. Hassan

Jami'an 'yan sandan dai na gudanar da ayyukan tsaro ne ga tawagar ma'aikatan kiwon lafiya da ke gudanar da aikin allurar rigakafin kwayar cutar Polio a kasar ta pakistan. Rahotanni sun nunar da cewa lamarin ya afku ne a garin Quetta da ke Kudu maso Yammacin kasar. Wani jami'in dan sanda a yankin da ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya shaidawa kamfannin dillancin labaran Faransa na AFP cewa daga cikin mutanen da suka rasun akwai jami'an 'yan sanda 12 da fararen hula biyu da kuma wani jami'in tsaron farar hula guda. Hukumomin kasar dai sun sanar da cewa sun fara gudanar da bincike domin gano wadanda ke da alhakin kai harin.