Hari kan jami′an tsaro a kasar Masar | Labarai | DW | 19.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan jami'an tsaro a kasar Masar

'Yan bindiga daga kungiyar tsagerun yankin Sinai na kasar Masar sun kai wani hari a shingayen duba ababen hawa guda biyu a kasar tare da hallaka wasu sojoji.

Hare-haren tsageru a Sinai

Hare-haren tsageru a Sinai

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Masar MENA ya ruwaito cewar harin da suka kai a kusa da garin Sheikh Zuweid ya haifar da musayar wuta tsakanin tsagerun da kuma jami'an tsaron kasar ta Masar inda akalla sojoji biyar suka rasa rayukansu.

Ko da a ranar daya ga wannan wata na Yuli da muke ciki ma dai kungiyar tsagerun yankin na Sinai da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'addan IS ta kai hari a wadannan shingayen duba ababen hawan, kana a farkon mako mai karewa ma sai da kungiyar ta kai wani hari a kan rundunar sojojin ruwa ta Masar din.