Hari kan hafsan hasoshin Somaliya | Labarai | DW | 10.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari kan hafsan hasoshin Somaliya

Kungiyar Al Shabaab ta yi yunkurin halaka babban jami'in sojin kasar Somaliya, a wani harin kunar bakin wake da ya halaka rayukan mutane goma.

Babban hafsan tsaron kasar ta Somaliya, ya tsallake rijiya da baya ne a wani harin bam da aka danganta da martanin kungiyar Al Shabaab da shugaban kasar ya bayyana daukar matakin fito-na-fito da ita.

Wani dan kunar bakin wake ne dai ya yi amfani da mota shake da nakiyoyi ya kutsa cikin ayarin motocin shugaban sojojin kasar Ahmed Mohamed Jimal, da aka nada ranar Alhamis da ta gabata. Kungiyar Al Shabaab dai bata yi wata-wata ba wajen daukar alhakin harin da ta kai kusa da shelkwatar tsaro da ke Mogadishu babban birnin kasar.

Wani babban jami'in soja Mukhtar Adan Mo'allim, ya shaidawa kamfanin dillancin labaransa Faransa AFP cewa wasu jami'an soji uku ma sun halaka a harin. Wannan dai shi ne sabon harin da kungiyar ta kai a kasar bayan wani na bam din da ta kaddamar ranar Larabar makon jiya, inda mutane 7 suka mutu.