Hari akan masu boren adawa da gwamnatin Masar | NRS-Import | DW | 31.12.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Hari akan masu boren adawa da gwamnatin Masar

'Yan bindiga dadi sun bude wuta akan masu bore a dandalin Tahrir da ke zama cibiyar kifar da gwamnatin Mubarak.

Jami'an tsaron kasar Masar sun sanar da cewar wasu 'yan bindiga dadi rufe da fuskokinsu sun kutsa cikin dandalin Tahrir da ke tsakiyar alQahira, babban birnin kasar Masar, inda suka bude wuta akan masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Masar, tare da jiwa biyu daga cikin masu boren munanan raunuka. Hakanan suka ce wasu 'yan bindiga dadi hudu sun la'la'ta ababen hawan da ke yankin - ciki kuwa harda na ofishin jakadancin kasar Amirka a safiyar wannan Litinin. Jami'an dai sun sanar da hakanne - da sharadin sakaya sunayensu domin ba a basu umarnin yiwa manema labarai magana akan batun ba - a hukumance.

Ofishin jakadancin kasar ta Amirka ya sanar da cewar wasu bata-gari sun afkawa motar ofishin tare da huda tayoyinta da kuma fasa tagogin motar, inda kuma ofishin ya gargadi Amirkawa da su guji zuwa kusa da dandalin Tahrir, duk kuwa da cewar ofishin jakadancin na kusa da dandalin ne, inda aka tsara gudanar da bukukuwan sabuwar shekara - nan gaba kadan.

Idan za'a iya tunawa dai dandalin ne ke zama cibiyar boren daya kai ga kifar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak kimanin shekaru biyun da suka gabata, kana boren da ke gudana yanzu haka a can, na nufin nuna adawa da amincewa da sabon tsariin mulkin da shugaba Morsi na Masar ya yi ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 31.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Bl1
 • Kwanan wata 31.12.2012
 • Rahotanni masu dangantaka Masar
 • Muhimman kalmomi Masar
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Bl1