Hari a Ringim da ke Jigawa a Najeriya | Labarai | DW | 29.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hari a Ringim da ke Jigawa a Najeriya

Wani abu mai kama da bam ya fashe a wani hari da aka kai a gidan tsohon sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Hafiz Ringim a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa.

A daren jiya lahadi an kai wasu hare hare a karamar hukumar Ringim da ke jihar jigawa ta Tarayyar Najeriya, inda aka ji fashewar wani abu mai kama da bam da karar bindigogi. Wannan dai shi ne hari na farko a jihar jigawa tun bayan tabarbarewar al'amuran tsaro a arewacin tarayyar ta Najeriya.

Mazauna Ringim da wakiliyarmu Zainab Shu'aibu Rabo ta tuntuba sun bayyana cewar an kai harin ne a gidan tsohon sufeto janar na 'yan sanda Hafiz Ringim da ke makwabtaka da ofishin 'yan sanda da kuma gidan ministar ilmi forfesa Rukayya Ahmed Rufai. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda da ke Jigawa Abdu Jinjiri ya tabbbatar da harin. sai dai yaki ya bayyana wadanda ake zargi da kai shi

Kasancewar gwamna Suley Lamido ya yi balaguro zuwa kasar waje, mataimakin gwamnan wannan jiha zai yi wa manema labarai cikakken jawabi a wannan litinin. Ita ma rundunar 'yan sanda za ta yi karin haske akan asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh