Hare-haren ta′addanci sun karu a Masar | Siyasa | DW | 20.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hare-haren ta'addanci sun karu a Masar

Kungiyar IS ta dauki alhakin tayar da bama-bamai a dab da ofishin jami'an leken asirin Masar da kuma wata kotu. Harin da- ya zuwa yanzu-mahukunta suka ce ya jikkata a kalla mutane 29.

Birnin Alkahira, mai mutane sama da miliyan 20 ya wayi gari da jin karar fashewar wasu abubuwa masu tsananin kara, wadanda mahukunta suka ce, bama- bamai ne da aka dana a motoci, suka tashi a gefen ofishin jami'an leken asirin kasar da kuma wata kotu a unguwar Shubrah da ke gundumar Qailubiyyah. Hare-haren da suka ritsa da mutane 29, cikinsu har da jami'an tsaro, ko da yake har yanzu babu rayin da aka ce ya salwanta

Yadda abin ya kasance a zahiri

Wani daga cikin wadanda suka fara isa wurin da harin ya auku ya bayyana abin da ya ganewa idonsa:

"Da muka iso,mun ga wani sanye da riga mai ruwan dorawa ya yana guda,kana yah au kan mashin ya tsere. A kasa kuma, mun tarar da mutane a kwankwance jina jina. Wani hanu da kafarsa sun tsinke. A gefe daya kuma ga wani wagegen rami, daura da yadda motar da ta fashe.

Ägypten Bombenanschlag in Kairo

Mutane da dama sun yi rauni

Kungiyar Ansarul Baitil Maqdis da ta yi mubaya'a a kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin a sakon da ta baza a shafinta na tweeta, yadda ta ce, ta kai hare-haren ne don martini da zartar da hukuncin kisa a membobinta 6 da aka yi a watan mayun da ya gabata.

Martanin shugaba Al-Sisi

Wadannan hare-hare dai na zuwa ne, kwanaki biyu bayan da shugaban kasar, Abdulfattah Sisi ya rattaba hannu kan dokar ta'adanci, wacca ta ba wa jami'an tsaro da alkalai ikon da ya wuce kima, lamarin da ya sanya masharhanta ke wa hare-haren fassara daban daban

"Na yi ammanar cewa akwai sakon da wadannan hare hare ke dauke da su, musamman ga baki 'yan kasashen waje da ke da aniyar sanya hannun jari a mashigin ruwa na Suez, da kuma masu sha'awar yawan shakatawar da ya dan fara murmurewa a yan watanin nan. Kuma gargadi ne ga baki yan kasashen Yamma da ke zaune a nan kasar"

Bombenanschlag in Kairo

Har da jami'an tsaro daga cikin wadanda suka hallaka

Shawara kan hanyar yaki da ta'addanci

Shi kuwa Imad Mubarak, memba a jam'iyar Ahrar Masar cewa ya yi, hare-haren sako ne ga mahukunta cewa, ba ta yadda za'a iya magance ayyukan ta'addanci ta hanyar amfani da tsagwaran karfi ko sanya dokoki:

"Murkushe ta'addanci batu ne da ke bukatar bin matakai mabanbanta. Rufa- rufa da gwamnati take kan wannan yaki da ta'addanci a yankin Sinai, da kuma sanya illahirin yan adawar siyasa cikin yan ta'adda, na kara sanya ayyukan ta,addanci su ta'azzara ne. Wadannan hare-haren ta'addanci sako ne, cewa, kurarin da gwamnati take na iya murkushe 'yan ta'adda da karfin tuwa mafarki ne. Ana iya yakar ta'addanci ne ta bin hanyoyin daban-daban, kama daga bin matakan tsaro da wayar da kan jama 'a, gami da daukar matakan siyasa"

Sauti da bidiyo akan labarin