Hare-haren sun hallaka jami′in diplomasiya na Iran | Labarai | DW | 19.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren sun hallaka jami'in diplomasiya na Iran

Hare-haren kunar bakin sun hallaka mutane 23 kusan da ofishin jadancin Iran a Lebanon

Jami'in diplomasiya na kasar Iran na cikin mutane 23 da suka hallaka sanadiyar tagwayen hare-haren kunar bakin wake, kusa da ofishin jakadancin kasar ta Iran da ke Beirut babban birnin kasar Lebanon. Akwai wasu mutane kimanin 150 da suka samu raunika.

Jakada Ghazanfar Roknabadi ya tabbatar da mutuwar Ibrahim Ansari jami'in diplomasiya, bayan hare-haren bama-bamai da aka kai da mota da kuma babur.

Tuni mahukuntan birnin Teheran na Iran suka zargi Isira'ila da hannu cikin farmakin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu