Hare-haren rundunar Isra´ila a zirin Gaza | Labarai | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren rundunar Isra´ila a zirin Gaza

Rundunar Isra´ila ta kai wasu sabin hare-hare a zirin Gaza, inda a nan take mayaƙa 3, na ƙungiyar Djihad Al Islami su ka rasa rayuka.

Kakakin ƙungiyar Fatah Al Islami, ya nunar da cewa, wannan hari ko mici ƙala zaratin, ba zai sa su yi ƙasa a gwiwa ba, a niyar su ta ƙwatar yancin Palestinu.

Wannan hari, ya zo kwana ɗaya rak, bayan da Isra´ila ta kashe wasu magoya bayan Hamas su guda 6 a zirin na Gaza a cikin wani harin rokoki.

Isra´ial ta maitsa ƙaimi wajen kai hare hare a zirin Gaza tun lokacin da yankin ya shiga hannun yan ƙungiyar Hamas.