Hare-haren kunar bakin wake a Masar | Labarai | DW | 07.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren kunar bakin wake a Masar

Majiyoyin tsaro a Masar sun ce an kashe sojoji 26 a wasu hare-hare na kunar bakin wake da wasu 'yan tarzoma suka kai da motoci a wasu wurarran bincike a yankin Sinai.

Rundunar sojojin ta Masar ta ce ta tura motocin daukar masu jiya a kudancin Rafah kan iyaka da yankin Gaza inda lamarin ya faru, sannan kuma ta ce sun kashe wasu mayakan na IS guda 40. Ya zuwa yanzu dai babu wani karin haske da rundunar sojojin ta bayar.