hare-haren Isra´ila a zirin Gaza | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

hare-haren Isra´ila a zirin Gaza

Rundunar Isra´ila, ta kai sabin hare-haren a zirin Gaza, wanda su ka hallaka a ƙalla Palestinawa 6.

Daga ranar asabar da ta wuce, zuwa yanzu, Isra´ila ta kashe mutane 13 a wannan ziri, wanda ke cikin kular ƙungiyar Hamas.

Isra´ila ta kai wannan hari, da zumar rugurguza wata cibiyar makamai, mallakar ƙungiyar Hamas.

Kazalika,sojojin bani yahudu, sun kutsa kai, a yankin Beit Hanoun da ke arwarcin zirin Gaza, inda su ka fuskanci turjewa daga mayaƙan Hamas.

Praminstan Isra´la Ehud Olmert, ya bayyana cewar dakarun sa, za su ci gaba da kai wannan hare-hare akai akai, domin ladabtar da ƙungiyar Hamas.

A sahiyar yau, dubbunan jama´a su ka shirya zanga-zangar lumana, azirin Gaza, inda su ka buƙaci ƙungiyoyin Hanas da Fatah su hau teberin shawara, domin kawo ƙarshen rikici tsakanin su, wanda a halin yanzu ya hadasa rabuwar Palestinu gida 2.