Hare-haren Isra´ila a Naplouse | Labarai | DW | 16.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-haren Isra´ila a Naplouse

Rundunar Isra´ila, ta kai sabin hare-hare a birnin Naplouse, da ke yamma ga kogin Jordan.

Kakakin rundunar, ya nunar da cewa, harin ya hadasa mutuwar mutum ɗaya, da kuma jima wani ƙarin ɗaya rauni.

Wanda ya rasa ran, na ɗaya daga magoyan bayan Rundunar mayaƙan Al Aksa, mai biyyaya ga shugaban hukumar Palestinawa Mahmud Abbas.

Wannan hari ya zo daidai lokacin da gwamnatin Isra´ila ta lashe amen ta, a game da alƙawarin belin ƙarin wasu pirsinoni na Fatah.

Idan ba a manta ba, ranar 20 ga watan juli, Isra´ila ta saki pirsinboni 250 na ƙungiyar Fatah, daga jimlar Palestinawa dubu 11 da ke tsare a kurku.

Ta kuma alƙawarta ci gaba da sallamar wasu, a wani mataki na ƙara ƙarfin gwiwa ga Mahamud Abbas, da ke fuskantar ƙalubalen ƙungiyar Hamas.