Hare-hare sun hallaka mutane 29 a Buni Yadi | Labarai | DW | 25.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare sun hallaka mutane 29 a Buni Yadi

Wasu masu gwaggwarmaya da makamai da aka danganta da Boko Haram sun hallaka mutane 29 a kwalejin gwamnatin tarayya da ke garin Buni Yadi na jihar Yoben Najeriya.

Wasu 'yan bindiga da aka danganta da 'ya'yan Ƙungiyar da aka fi sani da sunan Boko Haram sun kai hari a kwalejin da ke garin Buni Yadi a jihar Yoben Najeriya inda suka kashe mutane aƙalla 29. Wani babban jami'in tsaron jihar ta Yobe wato Sanusi Rufa'i da ya bayar da wannan labarin bai bayyana ko gaba ɗayan waɗanda harin ya ritsa da su dalibai ne ba, ko kuma har da malaman makarantar a ciki . Sai dai majiyar sojin Najeriya ta nunar da cewar a daren Litinin zuwa Talata ce wannan al'amari ya faru.

Rahotannin da ke zuwa mana daga jihar ta Yobe sun nunar da cewar an kashe wasu mutanen ne ta hanyar yankawa, yayin da wasu kuma suka ƙone ƙurmus bayan maharan sun ƙona makarantar garin Buni Yadi. Ko da shi ke dai Ƙungiyar Boko Haram ta yi ƙaurin suna wajen yin gwaggwarmaya da makamai a yankin Arewa maso gabashi Najeriya, amma kuma har yanzu ba ta fito fili ta ɗauki alhakin wannan hari ba na Buni Yadi ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane