1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare na kassara yaki da Ebola

Yusuf Bala Nayaya
October 23, 2018

Ma'aikatan agaji da ke yaki da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na fiskantar kai hare-hare sau uku ko hudu a duk mako a wannan kasa da ake ci gaba da samun labaran cutar Ebola a cikinta.

https://p.dw.com/p/36zMm
Kongo Ebola
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Mednick

Jagoran shirin yaki da wannan cuta ta Ebola a Kwango Dr. Ndjoloko Tambwe Bathe, ya fada wa manema labarai cewa hare-hare da ma'aikatansu daga ma'aikatar lafiya ke fiskanta daga 'yan tawaye da masu zanga-zanga ya sanya an tsayar da aikin yaki da wannan cuta ta Ebola a yankin da cutar ke kamari.

A wani hari guda ranar daya ga watan Agusta ma'aikatan lafiyar biyu da ke aiki da sojojin kasar ta Kwango 'yan tawaye sun halaka su, haka zalika kwana guda bayan wannan 'yan tawayen sun halaka fararen hula 15 a yankin Beni lamarin da ya jawo zanga-zangar al'umma da suka yi amfani da damar wajen ruwan duwatsu ga motar ma'aikatan lafiyar masu yaki da cutar ta Ebola.

Mutane 203 dai suka kamu da cutar ta Ebola yayin da 120 suka halaka tun bayan barkewar cutar ta Ebola a Kwango.