Hare-hare a kan wani asibiti a Libiya | Labarai | DW | 12.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a kan wani asibiti a Libiya

Mutane uku suka mutu kana wasu bakwai suka jikkata a cikin wani harin kunar bakin wake da aka kai a kan wani asibitin da ke a birnin Syrte na Libiya.

Majiyoyin tsaro sun ce harin ya yi kaca-kace da asibitin tare da haddasa asara mai yawan gaske.Sojojin masu yaki da Kungiyar IS wadanda galibinsu 'yan asilin garin Misirata ne da ke a yankin yammancin Libiyar na kalubalantar masu kai harin kunar bakin wake na Kungiyar IS.

Kuma kawo yanzu an kashe 120 daga cikin sojojin yayin da wasu 500 suka jikkata. a sumamen da Kungiyar IS ta ke kai musu ba dare ba rana.