Hare hare a Iraqi | Labarai | DW | 18.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare hare a Iraqi

Wani bam na cikin mota ya fashe kusa da wurin leburoru suke aiki a bakin wani masallacin yan shia a garin Kufa,inda mutane 43 suka rasa rayukansu wasu 65 kuma suka samu rauni.

Rahotannin sunce matasa da dama sunyi ta jifan yan sanda da suka isa yankin da bam din ya fashe,inda ana nasu bangare kuma yan sandan suka harba bindigogi akan matasan.

Wani wanda ya ganewa idonsa yace akalla mutane 2 suka samu rauni daga harbe harben yan sandan.