Hare-hare a birnin Teharan na Iran | Labarai | DW | 07.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a birnin Teharan na Iran

An samu wasu rahotanni na kai harin kunar baki kusa da kabarin jagoran juyin juya hali Ayatollah Khomeini

Wasu 'yan bunduga sun kai hare-hare a birnin Tehran fadar gwamnatin Iran kamar yadda kafafan yada labarai na kasar suka bayyana.

Akalla mahara uku ne suka kai farmaki majalisar dokokin kasar a tsakiyar birnin inda mutane uku suka ji raunika. A cewar kamfanin dillancin labarai na ISNA mutane ne dauke da bindigogi suka kutsa kai majalisar, wani dan majalisa ya fada wa kamfanin dillancin labaran IRNA cewa an kama daya daga cikin 'yan bindigar, kuma tuni aka rufe majalisar.

Har ila yau an samu wasu rahotanni na kai harin kunar baki kusa da kabarin jagoran juyin juya hali Ayatollah Khomeini.