Hare-hare a binin Bagadaza na kasar Iraki | Labarai | DW | 17.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a binin Bagadaza na kasar Iraki

Mutane da dama sun rasa rayukansu a wasu jerin hare-hare da 'yan bindiga suka kai a tsakiyar birnin Bagadaza. Babu kungiya da ta dauki alhaki har ya zuwa yanzu.

Akalla mutane 14 sun rigamu gidan gaskiya a Iraki yayin da wasu 55 suka jikata, a wasu jerin hare-hare da aka kadamar a Bagadaza babban birnin kasar. Hukumomin Tsaro da kuma na kiwon lafiya sun bayyana cewar wannan danyen aikin ya afku ne a dandalin Wathba da kuma na dandalin tayran da ke tsakiyar birnin Bagadaza.

Babu dai wata kungiya da ta fito ta dauki alhakkin wadanan tagawayen hare-hare. Amma kuma an saba dabgantasu da wadanda masu kaifin kishin addini na Is suka saba kaiwa tun bayan da suka maye wani bangare na Iraki.

Dakarun gwamnatin Iraki da ke da goyon bayan sojojin kawance da Amirka ke jagoranta sun yi nasarar kwato iko wasu sassa na kasar daga hannu masu gaggwarmaya da makamai. Sai dai kuma harn yanzu 'yan Is na ci gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba a yammacin kasar ta Iraki.