Hare-hare a Bajoga da Ashaka na Gombe | Labarai | DW | 04.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hare-hare a Bajoga da Ashaka na Gombe

Da safe ne 'yan bindiga suka kai hare-hare a cibiyoyin 'yan sanda na Bajoga kafin su durfafi Ashaka inda a watan Nowamba suka dauke nakiyoyin fasa duwatsu.

Mazauna garin Bajoga na jihar Gombe da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewar wasu 'yan bindiga sun kai hari a garin a yau Alhamis, inda suka lalata cibiyoyin 'yan sanda da na jam'iyyun siyasa tare da fasa bankuna.

Kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa 'yan bindigan sun kutsa garin ne da ayarin motoci 20, kuma sanye ne kakin soje. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan asaran rayuka. Sai dai shaidu sun nunar da cewa an shafe sa'o'i uku ana bata-kashi tsakanin 'yan bindigan da kuma jami'an tsaro.

Sai dai kuma daga bisani maharan sun durfafi Ashaka da ba shi da nisa da Bajoga, inda a watan jiya na Nowamba ma suka kai farmaki a masana'antar siminti. Idan za a iya tunawa dai yayin wannan harin sun yi awon-gaba da nakiyoyin da ake fasa duwatsun yin siminti da su.