Harbi a kan ′yan gudun hijira a Ukraine | Labarai | DW | 18.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harbi a kan 'yan gudun hijira a Ukraine

Dakarun gwamnatin Ukraine da 'yan aware gabashin kasar na ci gaba da zargin junansu da kai hari kan jerin motocin 'yan gudun hijira a kusa da birnin Luhansk.

Dakarun sojen Ukraine sun zargi 'yan Awaren gabacin kasar da harba wani makami mai linzami a kan jerin motocin 'yan gudun hijirar kasar kusa da birnin Luhansk. Sai dai tuni daya daga cikin jagororin 'yan awaren ya karyata inda ya ce dakarun na Ukraine ne suka yi wannan harbi.

A cewar wani kakakin sojen kasar ta Ukraine, wannan hari ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawan gaske, wadanda ba'a kai ga tantance yawansu ba. Fashewar abu mai karfin gaske ta haddasa konewar mutane da dama kurmus. Akalla dai dakarun sojan Ukrainetara ne suka mutu sakamakon fadan da ya wakana a daren jiya Lahadi zuwa wayewar yau Litinin.

A kowace rana dai daruruwan mutane ne ke tserewa daga birnin Luhansk daya daga cikin garuruwan dake hannun 'yan awaren kasar ta Ukraine inda a halin yanzu kusan babu ruwa da ma lantarki a birnin.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe