1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Harbe-harbe a yankin Buea

Yusuf Bala Nayaya
July 9, 2018

Wadanda suka sheda lamarin sun ce tun da sanyin safiyar Litinin ce suka fara jin karar harbe-harbe a yankunan Molyko da Malingo da Bonduma.

https://p.dw.com/p/314tt
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

A wannan rana ta Litinin an jiyo karar harbe-harbe a yankin Buea na kasar Kamaru da ya yi suna wajen samun tashin hankali tsakanin masu magana da harshen Ingilishi na kasar ta Kamaru da Jami'an tsaro kamar yadda wadanda suka sheda lamarin suka tabbatar.

Wadanda suka sheda lamarin sun fada wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa tun da sanyin safiyar Litinin ce suka fara jin karar harbe-harbe a yankunan Molyko da Malingo da Bonduma. A cewar wani da ya sheda lamarin wasu masu neman awaren ne suka shiga yankunan birnin inda suka rika harbe-harbe, yayin da sojoji da 'yan sanda suka mayar da martani.